4 Ku kuɓutar da talakawa da matalauta, Ku cece su daga ikon mugaye!
4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.
Domin sa'ad da matalauta suka yi kuka, ni nake cetonsu, Nakan taimaki marayu waɗanda ba su da mai taimako.
Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa, Da hakkin matalauta.
Haka Ubangiji ya ce, ka yi gaskiya da adalci, ka ceci wanda ake masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka cuci baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, kada kuma ka zubar da jinin marasa laifi a wannan wuri.