A ranar murnarku, da lokacin ƙayyadaddun idodinku, da tsayawar watanninku, za ku busa kakakin a lokacin yin hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama. Za su zama sanadin tunawa da ku a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
A farkon kowane wata sai a miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da kuma 'yan raguna bakwai bana daya daya; marasa lahani,