Ga abin da Ubangiji ya ce, “Raira wa Yakubu waƙar farin ciki da ƙarfi, Ku ta da murya saboda shugaban al'ummai, Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci jama'arka, Wato ringin mutanen Isra'ila,’
“Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah Don ya sami zaman lafiyarsa ba. A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa. Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”
ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin 'yan'uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa'ad da suka yi magana da shi.