Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna, da tsuntsayen sararin sama, da kowace irin dabba da take cikin saura, amma ba a sami mataimaki wanda ya dace da mutumin ba.
Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”
Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.”