5 Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi, Ka naɗa shi da daraja da girma!
5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
Kā sa shi ya gaza mala'iku a ɗan lokaci kaɗan, Kā naɗa shi da ɗaukaka da girma, Kā ɗora shi a kan dukkan halittarka.
Amma muna ganin Yesu, wanda a ɗan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, an naɗa shi da ɗaukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa. Wannan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.
Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako.
a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma.
Ya cece ni daga kabari, Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.
Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.
Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku, Ku da kuke biyayya da umarnansa, Kuna kasa kunne ga maganarsa!
Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin! Kana mulkin mallakarka da adalci.
Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don ya aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Ya kuma sāke aikawa, Yowab kuwa ya ƙi zuwa.
“Ya Ubangiji, me ya sa mutum yake da daraja haka a gare ka? Me ya sa kake lura da abin da yake yi?
Ya Ubangiji wane ne mutum, har da kake lura da shi? Wane ne ɗan adam kurum, har da kake kulawa da shi?