Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zabura 8:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Yara da jarirai suna raira shi, Ka gina kagara saboda magabtanka, Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zabura 8:2
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, “ ‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”


Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.


Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah, Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma, Maɗaukaki kuma a duniya!”


Amma Allah ya zaɓi abin da yake wauta a duniya, domin ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abin da yake rarrauna a duniya, domin ya kunyata ƙaƙƙarfa.


A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.


A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.


Saboda dukan wulakanci, Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.


“Amma Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Bari duniya ta yi tsit a gabansa.”


Tsoro da razana sun aukar musu, Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse, Har jama'arka, ya Ubangiji, suka haye, I, jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,


Ya kawo halaka a kan ƙarfafa, Da a kan birane masu garu.


Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku, Ku yi tunani da gaske a kan wannan A kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.


“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.


Amma ko kare ba zai yi wa wani mutum ko dabba na Isra'ila haushi ba, domin ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masarawa da Isra'ilawa.’


Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni, Damuwa ta fi ƙarfina. Sun yi wushefe a kan hanyata, Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.


Bari dukansu su yabi sunan Ubangiji, Sunansa ya fi dukan sauran sunaye girma, Ɗaukakarsa kuwa tana bisa duniya da samaniya!


Suna ta kiran junansu suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne! Ɗaukakarsa ta cika duniya.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ