Idan mutanen Isra'ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra'ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.”
Ga'al, ɗan Ebed, ya ce, “Wane ne Abimelek har mu mutanen Shekem za mu bauta masa? Ashe, ba Yerubba'al ne mahaifinsa ba, Zebul kuma shugaban yaƙinsa? Don me za mu bauta masa? Ku yi aminci ga kakanku Hamor, tushen kabilarku!