“Ku tafi ku yi tambaya ga Ubangiji saboda ni, da jama'a, da dukan mutanen Yahuza a kan maganar littafin nan da aka samo, gama Ubangiji ya yi fushi da muƙwarai saboda kakanninmu domin ba su bi maganar littafin nan ba, har da za su yi dukan abin da aka rubuta mana.”
Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka,
Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.
Kamar yadda zaki yakan fito daga cikin kurmin Urdun, garin ya fāda wa babban garken tumaki, haka zan sa nan da nan su gudu daga gare ta. Zan naɗa wani wanda na zaɓa, gama wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Ina makiyayin da ya isa ya yi gāba da ni?