2 Wurin zamansa yana Urushalima, A dutsen Sihiyona zatinsa yake.
2 Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.
Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki.
Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa! Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne, Yana zaune tare da mutanensa.”
Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama'ata Isra'ila.’
Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona, Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai. Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye Asabar Su ƙare a Sihiyona, Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.
A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa, Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa, Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.
Ku yabi Ubangiji, shi da yake mulki a Sihiyona! Ku faɗa wa kowace al'umma abin da ya yi!
Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo, Mai kyan gani ne na Allah, Birnin babban Sarki. Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!