Zabura 76:12 - Littafi Mai Tsarki12 Yakan ƙasƙantar da shugabanni masu girmankai, Ya tsoratar da manyan sarakuna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.
Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.