Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”
Don sa'ad da nake zagawa, na duba abubuwan da kuke yi wa ibada, har ma na tarar da wani bagadin hadaya da wannan rubutu a sama da shi cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wanda kuke yi wa sujada ba a tare da kun san shi ba, shi nake sanar muku.
Ka amsa mini sa'ad da na yi kira, Ya Allah, madogarata! Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona. Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!