Katakan itacen al'ul na cikin Haikalin, an yi musu zāne mai fasalin gora da na furanni buɗaɗɗu. An rufe bangon daga ciki duka da itacen al'ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.