16 Ka halicci yini da dare, Ka sa rana da wata a wurarensu.
16 Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata.
domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.
Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai, Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.
Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi, Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,
Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.
Ni na halicci haske duk da duhu, Ni ne na kawo albarka duk da la'ana. Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.
Amma ni Ubangiji na ce, idan ban kafa alkawarina game da yini, da kuma game da dare, da ka'idodin da take mulkin sammai da duniya ba,