Dukan kayayyakin waɗannan jiragen ruwa ba su da amfani, tafiyarsu ba za ta yi nisa ba! Za a kwashe dukan dukiyar sojojin abokan gāba. Za ta yi yawa har sauran jama'a za su sami rabonsu. Ubangiji kansa shi zai zama sarkinmu, zai mallake mu, ya kiyaye mu.
Ya yi kasai da ransa har ya kashe Bafilisten, Ubangiji kuwa ya ba Isra'ilawa babbar nasara. Kai ma ka gani, ka kuwa yi murna. Me ya sa za ka ɗauki alhakin Dawuda, wanda bai yi maka laifin kome ba?”
Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.
Ba kai ne madawwami ba? Ya Ubangiji Allahna Mai Tsarki. Ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji, kai ne ka sa su su yi hukunci, Ya dutse, kai ne ka kafa su don su yi horo.