Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila, Ya kuma bar yi musu taimako A lokacin da abokan gāba suka zo. Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.
Da sojojin da suka ragu suka koma sansani, sai shugabannin Isra'ila suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa Filistiyawa suka ci mu yau? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo ya kasance tare da mu, ya cece mu daga ikon abokan gābanmu.”