Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?
Ka natsu a gaban Ubangiji, Ka yi haƙuri, ka jira shi, Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya, Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.
A ganinmu masu girmankai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suke yi ba, amma sukan jarraba Allah da mugayen ayyukansu su kuwa zauna lafiya.’ ”