Ubangiji ya ce, “Zan datse karusa daga Ifraimu, In datse ingarman yaƙi a Urushalima, Zan kuma karya bakan yaƙi. Sarkinki zai tabbatar wa al'umman duniya da salama, Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku, Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”
Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.
Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”