Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zabura 72:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ka sa su girmama ka Muddin rana tana haskakawa, Muddin wata yana ba da haske dukan lokaci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zabura 72:5
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”


Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada, Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa. Da ma dukan sauran al'umma su yabi sarkin, Dukan jama'a su roƙi Allah yă sa musu albarka, Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a cikin Ikkilisiya ta wurin Almasihu Yesu, har ya zuwa dukkan zamanai har abada abadin. Amin.


Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


A kullayaumin daga cikin zuriyarsa ne za a naɗa sarki, Mulkinsa zai dawwama kamar sararin sama.


Ka sa adalci ya bunƙasa a zamaninsa, Wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.


Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.


Sai Sama'ila ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa aka yi tsawa da ruwan sama a wannan rana. Dukan jama'a kuwa suka ji tsoron Ubangiji da Sama'ila ƙwarai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ