Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu, Domin ana zaluntar masu bukata, Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi. Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”
Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda ya yarda da kai, ya sa ka a kan gadon sarautar Isra'ila, domin Ubangiji yana ƙaunar Isra'ila har abada, ya naɗa ka sarki domin ka zartar da shari'a da adalci.”
Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”
“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.