12 Kada ka yi nisa da ni haka, ya Allah, Ka yi hanzari ka taimake ni, ya Allahna!
12 Kada ka yi nisa da ni, ya Allah; zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni.
Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan. Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji, Kada ka yi nisa!
Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki, Ya Allah, ka zo wurina da hanzari. Kai ne mataimakina da Mai Cetona, Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!
Kada ka yi nisa da ni! Wahala ta gabato, Ba kuwa mai taimako.
Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa? Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala?
Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji! Na fid da zuciya duka! Kada ka ɓuya mini, Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.
Ka zo ka fanshe ni, Ka kuɓutar da ni daga abokan gābana.
Ka cece ni, ya Allah, Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji! Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!