Domin a tabbace yake a Nassi cewa, “Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke, Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”
Bari waɗanda suka tsananta mini su sha kunya, Amma kada ka bar ni in kunyata. Bari su tsorata, Amma kada ka bar ni in tsorata. Ka aukar musu da ranar masifa, Ka hallaka su riɓi biyu!
Aka taimake su yin yaƙi da abokan gābansu, sai aka ba da Hagarawa da duk waɗanda suke tare da su a hannunsu, saboda suka yi roƙo ga Allah a cikin yaƙin, Allah kuwa ya amsa musu roƙonsu saboda sun dogara gare shi.
Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra'ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa.