3 Ka sa waɗanda suke mini ba'a Su razana sabili da fāɗuwarsu!
3 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su juye baya saboda kunyansu.
Ka sa waɗanda suke mini ba'a Su razana sabili da faɗuwarsu!
(To, shi mutumin nan, da ladan mugun aikinsa ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kā, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo.
“Ɗan mutum, da yake Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Madalla, Urushalima ta rushe, ƙofa ta buɗu, yanzu zan wadata da yake ta zama kufai,’
Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala,
Kada ka bar su su ce wa kansu, “Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!” Kada ka bar su su ce, “Mun rinjaye shi!”
Sukan zarge ni da kakkausan harshe, Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”
Ubangiji Allah ya ce, da yake maƙiya suna cewa, ‘Madalla, tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu,’
Ka sa a kori waɗanda suka tasar mini, A hallaka su! Ka sa a kunyata waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, A wulakanta su sarai!
Zan yi magana a kan adalcinka dukan yini, Saboda an yi nasara da waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, sun ruɗe.