1 Ka cece ni, ya Allah! Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
1 Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.
Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji! Na fid da zuciya duka! Kada ka ɓuya mini, Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.
Kada ka yi nisa da ni haka, ya Allah, Ka yi hanzari ka taimake ni, ya Allahna!
Kada ka yi fushi har ka tsauta mini, ya Ubangiji! Kada ka hukunta ni da fushinka!
Ka zo ka fanshe ni, Ka kuɓutar da ni daga abokan gābana.