“Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra'ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka.
Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’
A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da yake cikin teku.
Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”