11 Allah alƙali ne mai adalci, Kullum kuwa yana kā da mugaye.
11 Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.
Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya, Ubangiji mai sakayya ne, mai hasala. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa. Yana tanada wa maƙiyansa fushi.
Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.
Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai, Dukan adalai kuwa za su yi na'am da shi.
Ya Ubangiji, kai ne alƙalin dukan mutane. Ka shara'anta mini bisa ga adalcina, Gama ba ni da laifi, ina kuma da kirki.
Sammai suna shelar adalcin Allah, Domin shi yake yin shari'a!