Lokacin da Dawuda yake magana da mutanen, sai Eliyab babban wansa ya ji, ya husata, ya ce wa Dawuda, “Me ya kawo ka nan? Wa ka bar wa 'yan tumakin nan a jeji? Na san rigimarka da taurinkanka, ka zo ne don ka yi kallon yaƙi.”
Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce, Raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi. Mu kuwa muna tsammani wahalarsa Hukunci ne Allah yake yi masa.