Ya kai, wanda kake begen Isra'ila, Mai Cetonta a lokacin wahala, Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar? Kamar matafiyi wanda ya kafa alfarwarsa a gefen hanya don ya kwana, ya wuce?
Kada ka ɓoye mini fuskarka, ya Ubangiji! Kada ka yi fushi da ni, Kada kuwa ka kori bawanka. Kai ne kake taimakona, tun dā ma, Kada ka bar ni, kada ka yashe ni, Ya Allahna, Mai Cetona!