Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba'a, da la'ana a dukan wuraren da zan warwatsa su.
sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.
Ya ku firistoci masu miƙa hadayu a bagaden Ubangiji, Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka! Ku shiga Haikali, ku kwana, Kuna saye da tufafin makoki, Gama ba hatsi ko ruwan inabi da za a yi hadaya da su, A cikin Haikalin Allahnku.
A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa.