Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi, Zan kasance tare da ku, Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba. Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba, Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.
Adalci ne zai zama igiyar gwajin tushen ginin, aminci kuma zai zama shacin dirin ginin.” Hadirin ƙanƙara zai share dukan ƙarairayin da kuke dogara gare su, rigyawa za ta hallakar da zaman lafiyarku.