Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.
Ya Ubangiji, sa'ad da ka bar duwatsun Seyir, Sa'ad da ka fito daga jihar Edom, Ƙasa ta girgiza, Ruwan sama ya zubo daga sararin sama, I, gizagizai suka kwararo da ruwa.
Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.