Idan wani ya tashi tsaye don ya bi sawunka, ya kuma nemi ranka, Ubangiji zai kiyaye ranka, amma rayukan maƙiyanka za a wurga su kamar dutsen majajjawa.
Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.