18 Da ban watsar da zunubaina ba, Da Ubangiji bai ji ni ba.
18 Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;
Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.
Idan ka ƙi biyayya ga doka, Allah zai ƙi jin addu'o'inka.
Sa'ad da mutanen kirki sukan yi addu'a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.
Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.
“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.
Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.
Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta, Gama saboda haka kake shan wannan tsanani, Don a tsare ka daga aikata mugunta.
Hakika Allah bai ji holoƙon kukansu ba, Allah Mai Iko Dukka kuwa bai kula da shi ba.