Duba a kan duwatsu, ƙafafun wanda yake kawo albishir, Wanda yake shelar salama! Ya Yahuza, ka yi bikin idodinka, Ka kuma cika wa'adodinka. Gama mugun ba zai sāke zuwa ya yi gāba da kai ba, An datse shi ƙaƙaf.
Sa'ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, 'yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa'adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”