Ka san zuciyata, Kakan zo gare ni da dare, Ka riga ka jarraba ni sarai, Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba. Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.
Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”
kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku.
Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.
Zai zo ya yi hukunci kamar wanda yake tace azurfa, ya tsarkake ta. Zai tsarkake firistoci, ya tace su kamar yadda ake yi wa azurfa da zinariya. A sa'an nan ne za su kawo wa Ubangiji hadayun da suka dace.