6 Ka ƙara wa sarki tsawon rai, Ka sa ya rayu dukan lokaci!
6 Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.
Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo, Da yawan kwanaki.
Albarkarka tana a kansa har abada, Kasancewarka tare da shi, takan cika shi da murna.
Ubangiji ya ce, “Nufina ne ya sha wahala, Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara, Saboda haka zai ga zuriyarsa, Zai yi tsawon rai, Ta wurinsa nufina zai cika.
Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji, Kai ne kake biyan dukan bukatata, Raina yana hannunka.
Kyautanka zuwa gare ni da bansha'awa suke, Kyawawa ne kuwa ƙwarai!