3 Kai ne kāriyata mai ƙarfi Da take kiyaye ni daga maƙiyana.
3 Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.
Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.
Cetona da darajata daga Allah ne, Shi ne ƙaƙƙarfan makiyayina, Shi ne mafakata.
Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi, Kā kiyaye ni cikin yaƙi.
Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.
Yakan kasa kunne gare ni, A duk lokacin da na yi kira gare shi.
Ubangiji ne Mai Cetona, Shi ne garkuwata mai ƙarfi. Allahna, shi ne yake kiyaye ni, Lafiya nake sa'ad da nake tare da shi, Yana kiyaye ni kamar garkuwa, Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.
A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa, Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa, Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.