da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa'ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka.
cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba.