5 Ba za a tuna da kai a lahira ba, Ba wanda zai yabe ka a can!
5 Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari?
Matacce ba ya yabon Ubangiji, Ko wanda ya gangara zuwa cikin kabari.
Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.
Wane amfani za a samu daga mutuwata? Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari? Ko matattu suna iya yabonka? Za su iya shelar madawwamin alherinka?
Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi, Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.
Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki.
Ya Ubangiji, sai yaushe za ka ji tausayinmu? Ka ji tausayin bayinka!
Sa'an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”