Ya Allahna, ka karkato kunnenka ka ji, ka buɗe idanunka ka ga yadda mu da birnin da ake kira da sunanka muka lalace. Ba cewa muna da wani adalci na kanmu shi ya sa muka kawo roƙe-roƙenmu ba, amma saboda yawan jinƙanka.
Ku kamar kakanninku kuke, kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba. Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku,” in ji Ubangiji Mai Runduna. “Amma kun ce, ‘Ƙaƙa za mu yi, mu koma gare ka?’
Amma ni, zan yi addu'a gare ka, ya Ubangiji, Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa, Sabili da muhimmiyar ƙaunarka, Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.