Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni. Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa! Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji!
Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah, Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki, In raira waƙar yabo a gare ka da garayata, Ya Allah, Allahna!