10 Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai, Amincinka kuma har sararin sammai.
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari.
Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai, Amincinka kuma ya kai sararin sammai.
Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya, Haka kuma girman ƙaunarsa yake ga waɗanda suke tsoronsa.
Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji, Ta kai har sammai, Amincinka ya kai sararin sammai.
Adalcinka, ya Allah, ya kai har sammai. Ka aikata manyan ayyuka, Ba waninka!
Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara. Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa, Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.
Zan yabe ka, mai tsarona, Allah ne mafakata, Allah wanda ya ƙaunace ni.