Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.
Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Amasa wanda daga baya ya zama shugaban talatin ɗin, sai ya ce, “Muna tare da kai, ya Dawuda ɗan Yesse! Allah ya ba ka nasara tare da waɗanda suke tare da kai! Allah yana wajenka!” Sa'an nan Dawuda ya marabce su, ya maishe su shugabanni a sojojinsa.