Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zabura 53:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Amma dukansu sun koma baya, Su duka mugaye ne, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai, Babu ko ɗaya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zabura 53:3
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya, Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”


Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.


Amma dukansu sun koma baya, Su duka mugaye ne, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai, Babu ko ɗaya.


Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, Ko wannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa, Hukuncin da ya wajaba a kanmu.


Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.


Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyarsa, fajiri kuwa yă yi ta fajircinsa, adali kuwa yă yi ta aikata adalcinsa, wanda yake tsattsarka kuwa ya yi ta zamansa na tsarki.”


Da yake kun san shi mai adalci ne, ku dai tabbata duk mai aikata adalci haifaffensa ne.


Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.


Da kuma waɗanda suka juya, suka bar bin Ubangiji, Waɗanda ba su neman Ubangiji, ba su kuma roƙonsa.”


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa, Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.


Sai dukan Isra'ilawa suka janye jiki daga wurin Dawuda, suka bi Sheba, ɗan Bikri, amma mutanen Yahuza suka manne wa sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ