Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
Abin da maƙiyana ke faɗa, Ba abin da za a yarda da shi ba ne, Su dai, so suke su hallakar kawai, Bakinsu kamar buɗaɗɗen kabari yake, Maganganunsu kuwa suna da taushi da kuma yaudara.
Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama'arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.
Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.
Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.
“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.
Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.
Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?