1 Ka kasa kunne ga kalmomina, ya Ubangiji, Ka kuma ji ajiyar zuciyata.
1 Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji, ka ji ajiyar zuciyata.
Ka ji addu'ata, ya Allah, Ka saurari kalmomina!
Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci, Yana kuma sauraron roƙonsu. Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”
Ka sa maganata da tunanina su zama abin karɓa a gare ka, Ya Ubangiji, Mafakata da Mai Fansata!
Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu'ata! Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana!
Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.
Ka kasa kunne gare ni, ya Ubangiji, ka amsa mini, Gama ba ni da ƙarfi, ba ni kuwa da mataimaki.
Ka kasa kunne ga roƙona, ni adalin mutum, Ka lura da kukana na neman taimako! Ka kasa kunne ga addu'ata, Gama ni ba mayaudari ba ne.
Kada ka zaci ni 'yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”
Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra'ila, Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka, Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.
Gama ta yi addu'ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓun motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne,