Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba, Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe. Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka, Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.
Ka ɗauke ni mana, mu gudu, Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka. Da yake kana nan za mu yi farin ciki, Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki. Ya dace a ƙaunace ka!
Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”