7 Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.
7 Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.
Haka zan warwatsa su Kamar yadda iskar gabas take yi, a gaban abokan gābansu, Zan juya musu baya, ba za su ga fuskata ba, A ranar masifarsu.’ ”
Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber.
Zai nutsar da jiragen ruwa mafi girma mafi kyau.
Gama sarki yana da rundunar jiragen ruwa a tekun Tarshish tare da na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku rundunar jiragen ruwa na Tarshish sukan kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai, da ɗawusu masu daraja.
Al'ummai suka ji suka yi rawar jiki, Tsoro ya kama mazaunan Filistiya.
Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya.