6 Tsoro ya kama su suka razana, Kamar mace wadda take gab da haihuwa.
6 Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda.
Naƙudar haihuwarsa ta zo, Amma shi wawan yaro ne, Bai fito daga mahaifar ba.
Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa suka razanar da shi, gaɓoɓinsa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna.
Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda.
Saboda haka suka gudu da almuru, suka bar alfarwansu, da dawakansu, da jakunansu, suka bar sansanin yadda yake, suka tsira da rayukansu.