5 Da suka gan shi sai suka yi mamaki, Suka tsorata suka gudu.
5 sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro.
Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”
Da sarakunan nan duka suka haɗa ƙarfinsu, sai suka je suka kafa sansaninsu a wuri ɗaya a bakin ruwayen Merom domin su yi yaƙi da Isra'ilawa.
Sarakunan duniya sun yi tayarwa, Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare, Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.