Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.
Sa'ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra'ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.
Zuciyar Sarkin Suriya kuwa ta ɓaci ƙwarai a kan wannan al'amari, don haka ya kirawo fādawansa, ya ce musu, “Wane ne wannan da yake cikinmu, yana goyon bayan Sarkin Isra'ila?”
Ƙaƙa za mu amsa wa manzannin da suka zo gare mu daga Filistiya? Za mu faɗa musu, cewa Ubangiji ya tabbatar da Sihiyona, jama'arsa da suke shan wahala kuwa za su sami zaman lafiya a can.